Daga Hassan R Jibrin
Gwamnan jihar kanot Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon takwaransa Mallam Ibrahim Shekarau, murnar dawaiwa ga ainin gidansa na siyasa wato jam’iyyar APC.
Tsohon gwamna kuma tsohon Sanata,ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP wanda daya ne daga jiga-jiganta.
Baya ayyana ficewa da komawa APC, a fadar mundubawa, ya kuma bukaci magoya bayansa da su karbi katin jam’iyyar a mazabunsu.Wasu na ganin komawar ta Shekarau zuwa APC, mummunar dabara ce a siyasance, duba da ganin zuwa yanzu ‘yan majalisar tarayya ashirin da daya ne suka jefar da shaidarsu domin shiga jam’iyyar hadaka ta ADC.
Ce-ce-ku-cen da ayanzu ya kaure a birnin na Kano da kuma kafofin sada zumunta, wata alama ce mai sarkakiya dangane da ko Shekarau na na iya asarar wasu daga cikin magoya bayansa ko kuma za su amsa bukatar jagoran nasu duk da cewar, rikicin fidda Mataimakin Gwamna a yanzu nema yake ya jikawa APC bargo a cikin hunturun zaben 2027.










