Muhammad Chamama.

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan kalamansa da suka shafi ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur.

Mai ba Shugaban Ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke karɓa ba domin almubazzaranci ba ne, sai dai domin zuba jari a muhimman fannoni na tattalin arziki da za su kawo ci gaba.

A nasa ɓangaren, Muhammadu Sanusi II, wanda tsohon gwamnan Central Bank of Nigeria ne, ya nuna damuwa kan dalilin da ya sa gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur.

Sanusi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar News Central TV, inda ya bukaci a yi ƙarin bayani kan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati bayan sauye-sauyen tattalin arziki.

Lamarin na nuna ci gaba da muhawara tsakanin masana da shugabanni kan yadda ya kamata a tafiyar da tattalin arzikin ƙasa, musamman dangane da batun bashi da kuma cire tallafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here