Usman Labaran.
Mambobi Takwas na majalisar wakilai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) gabanin zaben shekarar 2027.
Thaddeus Attah (mazabar tarayya ta Eti-Osa, Legas), Usman Zubairu (mazabar tarayya ta Birnin Gwari/Giwa, Kaduna), da Sani Noma (mazabar tarayya ta Argungu/Augie, Kebbi) sun fice daga jam’iyyun Labour Party (LP), All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) da wasu Mutum Biyar sun fice daga jam’iyyun su zuwa ADC a Yau Talata.










