Daga Hassan R Jibtin.


Hukumar Ilmin Bai Daya ta jihar Kano,ta fitar da sanarwar gargadi ga wadanda suke wallafa sakamakon jarrabawarsu a shafukan sada zumuntar Facebook, da su daina domin kaucewa fadawa hannun ‘yan damfara ta yin amfani da bayanansu.


Daraktan Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Badamasi Danlami Jazuli, a madadin Shugaban Hukumar Mallam Yusuf Kabir, ya jaddada aniyar Hukumar da nuna fushinta ga duk wadda bai kiyaye wanna umarnin ba.


Tun farko an gargadi masu neman aikin da su guji yin hakan domin tsaron kansu.
A kwanakin baya ne, Hukumar ta sanar da daukar sabbin malaman makarantun firamare sama da dubu daya a fadin jihar, bisa tsarin nan na BESDA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here