Daga Hassan R Jibril.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawa da ta sahale masa wata sabuwar bukatar garzayawa Bankin Kasar Jamus, karbo bashin dala Miliyan 516, domin aikin hanyar Sakkwato zuwa Badagare dake Legas.
Idan ta tabbata, bashin Kasar zai karu daga dala biliyan 158 da miliyan 280 izuwa dala biliyan 158 da miliyan 796.
Masana tattalin arziki na yiwa Shugaba Tinubu kallon mai yunkutin baiwa kwangin talaucin samun gindin zama a Najeriya.
Kawo yanzu, takardar Naira sai cigaba take da shan makura a hannun kudaden kasashen waje, hatta Sidin Kasar Ghana yayi mata fintinkau a kasuwannin musayar kudade, idan aka kwatanta a kafin zaben 2023.










