Hassan Turaki.
Yanzu aka samu gagarumin sauyi a harkokin mulki a Karamar Hukumar Takai dake Jihar Kano, inda kansilolin karamar hukumar suka tsige sakataren su, daga muƙamin sa.
Rahotanni daga karamar hukumar takai sun bayyana cewa matakin tsige sakataren ya biyo bayan zarge-zarge da dama da kansilolin suka gabatar a kansa, ciki har da rashin gudanar da zaman majalisar zartarwa, tin daga lokacin da ya shiga ofishin sa da toshe duk wata kafa ta gudanar da F&GPC Meeting, da rashin iya mulki da kuma wasu matsaloli da suka shafi tafiyar da harkokin aikin karamar hukumar.
Wasu daga cikin kansilolin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da ingantaccen shugabanci da kuma kare muradun al’ummar Karamar Hukumar Takai.










