Abubakar Salihu.
Babbar Kotun Jihar Gombe ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekaru Biyar zuwa Biyu da rabi a gidan yari bayan an same su da laifin tono kabari tare da cire idanun wata gawa domin zargin yin tsafi.Alkalin kotun, Mai shari’a Abdulsalam Mohammed, ya yanke hukuncin ne bayan wadanda ake tuhumar Mohammed Isah (Chindo), Kawuni Sarki, Manu Saleh, Umar Jibrin (Daddy) da Adamu Nasiru duk daga kauyen Gadam a karamar hukumar Kwami, sun amsa wasu daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi musu.
A cewar mai gabatar da kara na jihar, Ahmed Yakubu Gombe, lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Satumba, 2025, lokacin da wadanda ake tuhumar suka shiga makabartar Musulmi ta Gadam da daddare, suka tono kabarin marigayi Malam Manu Wanzam, suka cire idanunsa biyu daga gawarsa. Har ila yau, ana zargin sun yi yunkurin tono wani kabari a makabartar a wannan rana.










