Ranar tashin alkiyama duk wasu halittu da duke bayan kasa Babu wanda ALLAH ya dora musu hukunce-hukunce kamar Dan adam.

Malam Nasir yahaya ne ya bayyana hakan yayin gabatar da tafsirin alqu’rani me girma da ya saba gabatarwa a kowace rana a babban masallacin juma’a na birnin Dutse.

Mal Nasir ya ce ranar tashin alkiyama bayan jama’ar duniya gaba daya sun taru a filin hisabi sai Kuma mala’iku su gewaye sansanin jama’a baki daya, inda mala’ikun za suyi sahu bakwai. Hakan na tabbatar wa alu’ma cewa babu karfi babu dabara dole ba inda mutum zai iya gudu dole ya tsaya a yanke masa hukunci dai-dai da abinda ya aikata a duniya.

A yayin wannan taron a filin hisabi ALLAH zai ce duk Wanda zai iya gudu ya nemi hanya idan zai iya, Babu wani Dan adam da zai iya temaka wa mala’iku haka Kuma babu wani mala’ika da zai iya temaka wa wani Dan adam.

A dai-dai wannan lokaci ana Sako harshen wuta me tsananin zafi zata dinga barazana wa masu yunkurin guduwa.

Babban malamin ya kara da cewa a irin wannan lokaci sama zata tsatstsage mala’iku su cigaba da saukowa yayin da sama zata kasance ja wanda shine kalar ta na asali idan aka cire hasken taurari da gajimare.

Malam Nasir ya kara da cewa babu wanda za’a tambaye shi abinda ya aikata a duniya saboda ALLAH ya riga ya san komai, sai dai za’ayi tambaya irin ta tursasawa wacce kai tsaye zata nuna wa kowa abinda yake aikatawa.

Da yake amsa tambaya, malamin yayi kira ga masu aiwatar da sallar asham cikin gaggawa da su kiyaye sallah cikin nitsuwa, ya tabbatar da cewa babu wata sallah da zata karbo idan ba’ayi ta cikin nitsuwa ba.

“Babu sallah idan anyi ta ba a cikin nitsuwa ba” kamar yadda malamin yace.

RPT/Hassan Turaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here