Our Reporter.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da wata manufa ta ƙara kuɗin wutar lantarki fiye da yadda yake a halin yanzu.

Ya ce abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai ba ƙara kuɗin lantarki ba ne, sai dai inganta samar da wuta, tabbatar da kowa ya samu na’urar auna amfani da wuta (meter), da kuma ganin ‘yan Najeriya suna biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita kaɗai.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nazarin ƙarin hanyoyin da za su kare masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu daga duk wani nauyi, tare da tabbatar da cewa bangaren wutar lantarki ya samu tsarin kuɗaɗen da zai sa ya dore.

A cewarsa, gyaran da ake yi wa fannin wutar lantarki ba magana ce ta siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba, illa aiwatar da tsare-tsare cikin tsari, haɗin kai da kuma auna sakamakon da ake samu.

Ya ce za a auna nasarar gyaran ne da irin sauyin da ‘yan Najeriya za su gani a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ministan ya ce burin gwamnatin tarayya shi ne samar da ingantacciyar wutar lantarki da za ta wadatar da gidaje, ta bunƙasa masana’antu, ta jawo masu zuba jari, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya amfana da ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here