Hassan Turaki.
Kungiyar kansilolin jihar Jigawa sun karrama gwamna Namadi da mota kirar BUS a matsayin kyauta ta musamman da sukayi wa gwamna domin jin dadin yadda yake tafiyar da mulkin jihar.
Da yake mika motar wa gwamna Umar Namadi Shugaban kansilolin jihar Jigawa Hon. Muhammad yakubu Gabarin yace tunda aka kafa jihar Jigawa ba’a taba samun gwamnan da yayi mata hidima ba kamar malam Umar Namadi.”Haka ne yasa muka yi yunkuri a matsayin mu na yayan ka, muka zo da wannan mota a matsayin kyauta ta barka da Sallah”. Inji Gabarin.
Haka zalika ya kara da cewa Dole muyi wa ALLAH godiya sakamakon bamu gwamna irin Namadi. Saboda kasancewar Namadi babban jami’in tsaron jihar Jigawa ne yasa jihar take kara kasancewa a matsayin jihar da tafi kowacce zaman lafiya a najeriya.
Shugaban tawagar kansilolin ya kara da cewa kansilolin jihar Jigawa sunyi alkawarin kawo masa kuri’un jihar a zaben shekarar 2027 ba tare da yaje kamfen ba.
Da yake jawabi yayin karbar tagomashin da kansilolin jihar suka yi masa, gwamna Mal. Umar Namadi ya yaba da kokarin su Kuma ya tabbatar musu cewa a shirye yake domin cigaba da aiwatar da ayyukan alheri a kowani sassan jihar domin tabbatar da sauke nauyin dake wuyar su a matsayin zababbu.
Sibu yace abin mamaki a nan shine “wadannan kansiloli sai da sukayi adashe sannan suka samu damar sayan wannan mota domin faranta ma gwamna a matsayin sa na Uba. Hakan ya nuna irin kokarin da gwamna yake yi wa alu’mar jihar, Inji shi.
Namadi ya kara da cewa, ya gamsu da kokarin da kansilolin jihar keyi kuma ya kara Jan hankalin su da su kara zage dantse wajen tabbatar da cigaba a yankunan su.Gwamnan ya kara da cewa abinda sukayi ya tabbatar masa da cewa yaya ne su na halali Kuma yayi kira da shugabannin kananan hukumomin jihar da su cigaba da rike su hanu bibbiyu.
Ya karkare da yi musu addu’ar fatan alkhairi.Yayin da yake nashi jawabin, shugaban kungiyar ciyamomin jihar Jigawa kuma shugaban karamar hukumar Dutse, Mal. Sibu Abdullahi yayi alkawarin isar da sakon gwamna ga kunnen duk shugabannin kananan hukumomin jihar 27 Kuma yace babu shakka zasu cigaba da rike wa gwamna amanar da ya basu na kula da kansilolin jihar Jigawa dama dukkannin al’umar dake karkashin su.










