Adamu Usman Raju.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar wazirin adamawa, ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaɓen Shugabancin Najeriya a 2027.
Waziri ya bayyana wannan matsayi ne a yayin wani Facebook Live, a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a ƙasar kan tasirin cire tallafin man fetur da kuma yadda matakin ya shafi rayuwar talakawan Najeriya.
A cewar Atiku, idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya, zai sake duba tsarin tallafin man fetur tare da ɗaukar matakan da zai sauƙaƙa wa ’yan Najeriya wahalhalun da ake fuskanta sakamakon tsadar man fetur.
Alƙawarin na Atiku na zuwa ne yayin da batun tallafin man fetur ya kasance ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da ke jan hankalin jama’a a siyasar Najeriya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.
Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya zartar a dai-dai lokacin da ya karbi ragama a shekarar 2023.
Gwamnatin ta ce matakin ya zama dole domin rage nauyin da tallafin ke ɗora wa tattalin arzikin ƙasa da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa wasu muhimman fannoni.
Sai dai masu suka na cewa cire tallafin ya ƙara tsadar rayuwa, musamman ta hanyar ƙarin kuɗin sufuri da farashin kayayyaki.










