Kabiru Bashir.
Mai Girma Manajan Darakta na Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are (HJRBDA), Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi, ya karɓi baƙuncin shugabanni da mambobin Kungiyar Tinubu, Abba, Barau Sako Sako a hedikwatar hukumar.
A yayin ziyarar, shugabannin ƙungiyar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi, tare da sanar da naɗa shi a matsayin Jagoran Ƙungiyar saboda irin nagartarsa, jajircewarsa wajen hidimtawa al’umma, da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi ya gode wa shugabanni da mambobin ƙungiyar bisa wannan karamci da amincewar da suka nuna masa. Ya bayyana cewa wannan naɗi ƙarin nauyi ne da zai ƙara masa ƙwazo wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.
An kuma tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙarfafa haɗin kai da kuma yadda ƙungiyar za ta ci gaba da shiga sako da lungu na jihohi da ƙananan hukumomi domin wayar da kan al’umma kan ayyukan ci gaba da manufofin Jam’iyyar APC a Kano da Najeriya baki ɗaya.
Haka kuma, an jaddada muhimmancin ci gaba da tallata nasarorin gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Shugaban Ƙasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR, musamman manufofin Renewed Hope Agenda, waɗanda ke da nufin bunƙasa tattalin arziki, inganta rayuwar al’umma, samar da ababen more rayuwa, da ƙarfafa ci gaban ƙasa.
Ziyarar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, haɗin kai, da ƙudurin ci gaba da aiki tare domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnati da ci gaban al’umma










