Daga Hassan R Jibrin.

Zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya amincewar da wani rahoto da Kwamatin Ilmi ya mika masa, bayan daukar dogon lokaci wajen ganawa da Kwamatin yayi da masu ruwa da tsaki a bangaren makarantu masu zanan kansu dake a fadin jihar dangane da yawan karin kudade barkatai.

Majalisar bayan karbar rahoton, ta kuma yiwa Dokar Gudanar da Makarantu Masu Zaman Kansu Dana Sa Kai kwaskwarima. Yanzu Hukunar dake sa ido akan makarantun, an samar mata da Ofishin Babban Sakatare, kuma ya zama wajibi ne ga makarantun da su nemi izinin Hukumar domin karin kudi a makarantun nasu.

Acewar Shugaban Majalisar, Rt Hon Isma’il Falgore, Dokar zata taimakawa iyayen yara da kare hakkin mu’amula a tsakanin su.

A wata sabuwa kuma, Majalisar ta dakatar da Shugabanin Kananan Hukummomin Rogo, Bebeji da Bagwai na tsawon watanni uku. Sanarwar dakatarwar bata yi karin haske kan dalilan ba.

Amma, ana iya ganin cewar ko hakan na da nasaba da binciken da a yanzu Majalisar ke gudanarwa akan Naira miliyan ashirin da ake baiwa Kananan Hukummomin a duk wata domin kula da fannin tsaro a yankunan nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here