Daga Hassan R Jibrin.

Tsohon wakilin Kananan Hukummomin Dawakin-Kudu da Warawa, a Majalisar Dokokin Tarayya, Hon Mustapha Bala Dawaki ( Maigidan Ruwa), ya jawo hankalin iyaye da masu kula da yara, da su kara zage damtse wajen goyon bayansu a fannin neman ilmin Al-Qur’ani Mai Tsarki, domin jigon rayuwar dan-Adam ne a duniya da lahira.

Shawarar ta biyo bayan halartar bikin saukar karatu da Madarasatul Abubakar Tahfez Qur’an K/Gabas Gano, a Karamar Hukumar Dawakin-Kudu dake jihar Kano ta gudanarAcewar sa, rashin ilmin addini yana taka rawa wajen tabarbarewar tarbiyya,talauci da rashin tsaro.

“Duk al’ummar da ta rasa ilmin addini za ta wayi gari da fuskantar barazanar rushewar tarbiyya, tausayi da kaunar juna”.Ita dai makarantar, dalibai 20 ne daga cikin 200 su ka samu damar shallake shinge akan sauka a tsawon shekaru biyar da kafuwar ta.

Malam Huzaifa Yahaya Abubakar, wanda shine shugaban makarantar, ya bayyana cewa, daliban na su, sun samu tarbiyar dake cikin Ak’Qur’ani.Ya kara da cewar, tsauraran matakan da su ka dauka kan haddar ya sa aka samu karancin mahaddatan.

“Babu gaggawa ko burgewa ga dalibi yayi hadda marar kwari” a cewarsa.Akarshe, Hon Mustapha ya bayar da gudunmawar naira dubu hamsin ga Makarantar da baiwa mahaddatan naira dubu biyar kowannensu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here