Hassan Turaki.
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana niyyar ta na ƙarfafa haɗin kai da Hukumar Horar da Masana’antu wato ITF, domin inganta ƙwarewa da ƙara ƙwazo ga ma’aikatan gwamnati a jihar.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ne ya bayar da wannan tabbaci yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin ofishin ITF na Jihar Jigawa, karkashin jagorancin Manajan ta, Injiniya Aliyu Zakari.
Dagaceri ya ce gwamnatin jihar ta amince da ƙwarewar ITF wajen baiwa ma’aikata horo, kuma tana ba da muhimmancin horar da ma’aikatan gwamnati.
Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta gajiya ba wajen ganin ma’aikatan gwamnati sun fi ƙwazo da aiki ta hanyar shirya horo na yau da kullum.
A baya dai Injiniya Zakari ya bayyana wa Shugaban Ma’aikata ayyukan ITF, inda ya ce an kafa hukumar ne domin inganta samun ƙwarewa a fannin masana’antu da kasuwanci, domin samar da ma’aikata ƙwararru da za su biya buƙatun ɓangarorin gwamnati da na masu zaman kansu.
Ya ce ITF ta horar da ma’aikata a faɗin ƙasar nan tare da samun sakamako mai kyau, kuma yace gwamnatin Jigawa a shirye take domin ta ƙarfafa haɗin kai da hukumar domin horar da ma’aikatan jihar.










