EDITA.
Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta sanar da dakatar da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Ibrahim Kamfani Auyo, tare da wasu jami’an jam’iyyar guda shida a ƙaramar hukumar Auyo.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar 31 ga watan Mayu, 2026, ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa zargin saba dokokin jam’iyya, da suka haɗa da cin amanar jam’iyya, haddasa rikice-rikice a cikin gida da kuma raba kan mambobinta.
Sauran waɗanda dakatarwar ta shafa sun haɗa da Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jiha, Aisha Adamu Auyo (Kande), Shugabar Mata ta Gundumar Auyo, Yargabi Babannan Auyo, Shugaban Gundumar Auyo, Musa Idris Zabarau, Mataimakin Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Auyo, Ibrahim Ayama, Sakataren Kuɗi na APC a ƙaramar hukumar, Saje Hadiyau, da kuma Mataimakin Shugaban Gundumar Auyo, Sani Abdullahi Hadiyau.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne ƙarƙashin jagorancin zababben Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa, Rt. Hon. Ahmad Garba MK, tare da jaddada cewa dakatarwar ta fara aiki nan take.
Jam’iyyar ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinta na tabbatar da bin ƙa’idoji da kare haɗin kan jam’iyyar a jihar.










