Daga Hassan R Jibrin

Duk da kasancewa sakamakon zaben fidda gwani a jam’iyyar ADC bai kammalu ba, guda daga cikin manema takarar shugaban kasa, Muhammed Hayatud-Deen, yayi watsi da kwarya-kearyar sakamakon zaben.

Ya shaidawa manema labarai cewar, zaben yana cike da magudin da ya wuce tunani, domin shi ganau ne.

“Rahotanni daga sassa daban-daban a fadin Kasa daga wakilai na sun kara jefa shakku dangane da sahihancin yadda ake gudanar da shi” a cewar Hayatud-Deen.

Ya kuma ce zai kauracewa taron sanar da sakamakon da uwar jam’iyyar za tayi.

Mutane uku ne ADCn ta sahalewa fafatawa don neman takarar Shugaban Kasa a inuwarta, wadanda suka hada da Wazirin Adamawa kuma tsohon Mataimakin Shugaba Kasa Alhaji Atiku Abubakar, tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Rotimi Ameachi da kuma shi Muhammadu Hayatud-Deen, tsohon dan-takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar Labour tare da Peter Obi a zaben 2023 .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here