Shehu Mustapha Chaji

An wayi gari da labarin Shugaban Kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kori Firaminista Ousmane Sonko da Ministoci talatin da biyar.Wannan abinda ya faru ya tashi hankalin masu bibiyar siyasar kasar Senegal.

Sonko shine ya dauko Faye ya bashi Jam’iyya ya kuma tsaya masa ya mara masa baya ya zama Shugaban Kasar Senegal.

Sonko shine Jagoran yan adawa kuma wanda kungiyoyin matasa a kasar Senegal suke son ya zama Shugaban Kasa amma kotunan Kasar suka haramta masa tsayawa takara.

Sonko ya hakura da takara ya dauko Faye ya saka a gaba suka kayar da gwamnatin Macky Sall.Bayan samun nasara Faye ya nada Sonko a matsayin Firaminista.

Sonko ya kasance yana tsananin adawa da manufofin bankin duniya da IMF da basusukan da suka bawa Kasar da yawan jawabai masu kaushi kan kasar Faransa da Kasashen Yamma da LGBT.

Wasu masu sharhi kan siyasar Kasar Senegal na ganin da hannun wasu daga wajen kasar wajen ganin an kori Sonko da kuma shi Faye yana ganin Sonko zai fito takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2029 wanda hakan barazana ne a gare shi.

Rikicin Sonko da Faye ya Kare nunawa duniya yanda ake yawan samun sabani tsakanin Ubangida da wanda ya dora a kan mulki.

Za’a cigaba da sa ido a gan yanda zata kaya tsakanin Sonko tsohon ubangidan Shugaba Faye yayin da kasar ke tinkarar zaben shekarar 2019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here