Ibrahim Aminu makama
Wani ɗan jarida da ke birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Sidi Chaibou, ya bayyana cewa rayuwarsa ta samu sauyi mai kyau tun bayan hawan Janar Abdourahamane Tiani kan mulki.
Chaibou ya ce ya shafe tsawon shekaru 15 yana aikin jarida, amma duk da ƙoƙarin da yake yi, bai taɓa samun damar biyan buƙatunsa yadda ya kamata ba sai a cikin gwamnatin Janar Tiani.
“Na yi shekaru 15 ina aikin jarida cikin wahalhalu da ƙalubale iri-iri.
A baya ina fama wajen biyan wasu muhimman buƙatu na rayuwa, amma tun bayan zuwan Janar Tiani abubuwa sun fara sauyawa zuwa alheri,” inji shi.
Ya ƙara da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin gwamnatin Nijar sun taimaka wajen bunƙasa rayuwar al’umma da dama, musamman ma’aikata da ‘yan kasuwa.
Chaibou ya yaba da irin matakan da gwamnatin Nijar ke ɗauka wajen ƙarfafa tattalin arziki da kuma bai wa ‘yan ƙasa damar cin gajiyar albarkatun ƙasarsu.




