Daga Hassan R Jibrin
A kwana a tashi, a sannu cikin hankali, damunar ta fara nuna alamun shigowa.
Wasu nanoman sun fara share gonakinsu bisa al’ada, tanadin iri domin shukawa, hakan na da daga cikin muhimman aiyuka ga manoma kanana da manyansu.
Taki, shine ruhin duk abin da yabanya ke bukata da ruwa. Sawa’un na zamani ko na gargajiy. Farashin takin zamani, kawo yanzu.ya haura Naira 40,000.
Tsadar taki da subutowar farashin amfanin gona, ta hanyar shigowa da gwamnatin tayi, a bangare guda abu ne alfanu,yayin da daya bangaren karya gwuiwar manoma ne.
Da kamata yayi gwamnati ta saye amfanin daga wajen manoman cikin gida, maimakon daga waje.Bincike ya nuna a duk buhun takin da manomi ya sa a gonarsa, yayi asarar rubu’in kudin.
Misali, idan kudin taki Naira 20,000 ne, to yayi asarar Naira 5000 ga yadda farashin amfanin ya rikito kasa !Ana ganin idan gwamnati bata yi wani tsari ingantacce ba, za’a samu raguwar manoma a damunar bana,Wanne shiri manoman ke yi ?










