Daga Hassan R. Jibrin.

Ministan Babban Birnin Tarayya Barista Nyesom Wike, ya umarci magoya bayan sa da su koma jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Umarnin Ministan yana da nasaba da cikekken bayanan da suke cikin sahihin kwafin shari’ar da Kotun Koli ta yanke dangane da rikicin jam’iyyar ta PDP.

Rashin samun galaba ga tsagin Wike, a shari’ar ba karamin koma baya bane ga jam’iyyar sakamakon rasa magoya bayan sa.

Baya ga haka, suma tsagin Turaki, duk da ba su sami nasara a hukuncin ba, a iya cewa ruwa ta sha, domin tsagin sune Kwamatin Dattawan jam’iyyar suka dorawa nauyin gudanar da shugabancin jam’iyyar a matsayin shugabannin rikon kwarya.

Tuni ta bayan fage Kakakin Majalissar Ribas ya bi Gwamna Similayi Fubura zuwa APC, wanda akewa ganin babban na hannun daman Ministan ne.

Komawar Wike cikin APC, ana iya cewa tsugune bata kare ba dangane da rikici tsakanin Gwamna Fubura da tsohon mai gidan nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here