Daga Hassan R. Jibrin.
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, kuma dan tsohon gwamnan jihar, Honarabul Mohammed Ahmed El-Rufa’i, yayi fatali da tayin tikitin takara na kai tsaye da Jam’iyyar sa ta APC ta bashi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an kwashe sa’o’i tara ana rarrashin sa domin amincewa, amma yayi kememe.
Ana danganta tayin da umarni daga fadar shugaban kasa a matsayin wani abu mai kama da danne kirji akan halin da mahaifin sa ke ciki.










