Daga Hassan R Jibrin.
Hausawa kan ce wata miyar sai a makwabta. Yayin da Najeriya ke laftowa ‘ya’yanta bashi da kuma fama da kunzugun rashin tabbas akan halin rayuwa.
Su kuwa kasashen Zambiya da Namibiya darawa suke yi acikin cikekken ‘yancin tattalin arziki.
Kasar ta Zambiya, ta nunawa Amurka cewar,su ba mabarata bane. Jakadan jasar Amurka a Zambiya, ya mika tallafin Dala biliyan daya.
Amma ministan kudin Zambiya yace akai tallafin ga mabukata,amma ba kasar su ba.
Ita kuwa kasar Namibiya,duk wani bashi ko lamuni da aka taba ciyowa kasar, ayanzu sun yar da kwallon mangwaro domin kaucewar kudaje.
Basussuka na shekaru fiye da arba’in, ayau babu wata Kasa ko bankuna daga waje ko na cikin gida dake binta bashi.
Tuni darajar takardun kasar ya fara yiwa dalar Amurka muzurai.
Lalle,su yaya babba ya kamata a dau darasi domin ‘yantar da al’ummomi ta a fannin tattalin arziki.










