Daga Hassan R Jibrin
Rahotanni sun tabbatar da cewa, jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya umarci magoya bayan sa da su bar jam’iyyar ADC zuwa NDC.
Ana ganin shima Peter Obi zai iya biyo Kwankwaso domin cimma muradun takara a kakar zaben 2027.
Rikicin cikin gida da yake neman kassara ADC ya sa dole Obi da Kwankwaso neman mafita a siyasar Najeriya 2027.
Duk da hukuncin Kotun Koli, hakan ba zai haifarwa ADC da mai ido ba.
Ragowar shari’un dake gaban Mai Shariya Nweti na Babbar Kotun Abuja da kuma Joyce Abdulmalik ta Kotun Daukaka Kara, babu wasu ranaku da su Ke bayyane domin kawo karshen su.
Ita kuwa INEC a cikin jadawalin da ta fitar kafin ranar 18/05/2026 ita ce karshe na karbar rajistar ‘yan-jam’iyyu daku masu sha’awar nuna kwanji a zaben na 2027.










