Hassan Turaki.
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin Doron Baga.
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun mamaye ƙauyen inda suka tara masuntan waje guda.
Majiyar ta ce “sun iso ne da makamai, inda suka yi barazanar tayar da hankali idan ba mu bar jiragen ruwanmu ba, daga nan ne ‘yan ta’addan suka ƙwace kwale-kwale guda takwas sannan suka tsere ta cikin kogin.
Leave a Reply