Ibrahim A. Makama.

‘Yan jam’iyyar ADC mazauna ƙasashen ƙetare sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a gaban ginin Majalisar Dokokin Burtaniya (UK Parliament) da ke birnin London a ranar Lahadi.Masu zanga-zangar sun kai takardar kuka ga gwamnatin Burtaniya, inda suke neman ta tsoma baki kan abin da suka kira barazana ga tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya.Yan jam’iyyar ta ADC sun yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai bin tsarin jam’iyya guda ɗaya kacal.A cewarsu, gwamnatin tana amfani da rarrashi da kuma matsin lamba wajen ganin ta raunana jam’iyyun hamayya da kuma daƙile muryoyin masu kushe manufofinta. Sun bayyana cewa hakan zai nakasa dukkan wasu matakai na sanya ido da bincike da tsarin dimokuraɗiyya ya tanada.Baya ga batun jam’iyya guda, masu zanga-zangar sun buƙaci Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Josh Amupitan, da ya yi murabus daga kan mukaminsa.Sun zargi Shugaban na INEC da nuna son kai da kuma rashin adalci wajen tafiyar da ayyukan hukumar, wanda a cewarsu hakan na iya shafan sahihancin zaɓuka masu zuwa a ƙasar“Ba za mu zuba ido ana ruguza dimokuraɗiyyar da aka sha wuya kafin a samar da ita ba,” in ji ɗaya daga cikin masu zanga-zangar.Masu fafutukar sun roƙi ƙasashen duniya, musamman Burtaniya, da su sanya idanu sosai kan harkokin siyasar Nijeriya don tabbatar da cewa ba a karkata daga turbar adalci da bin doka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here