Daga Hassan R Jibrin.
Kamar yadda kafar Zuma News ta ruwaito, mai da’awar shugabancin jam’iyyar ADC na kasa,Alhaji Nafi’u Bala Gombe, da wasu magoya bayan sa na shirin tsunduma cikin jam’iyyar APC a kowanne lokaci daga yanzu.
Idan hakan ta tabbata, zargin da wasu kewa Alhaji Nafi’un ka iya kasancewa gaskiya ne wajen yunkurinsa na kawo tarnaki a cikin hadakar ADC.
Tsagin Nafi’u Gombe sun shirya gudanar da taron su na kasa a filin wasa na Cif Moshood Abiola dake Abuja, rashin halartar wakilai daga sassan Najeriya, ya hana gudanarwar.Ana ganin ko shirin shiga APCn ne ya hana taron ko kuma wani irin salo ne na siyasa.










