Daga Hassan R Jibrin.
Rahotanni na baya-bayan sun tabbatar da cewar dandalin filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja ya kasance fayau, saboda rasa samun halartar wakilan jam’iyyar ADC tsagin Nafi’u Bala Gombe don gudanar da taron kasa.
Ganau sun tabbatar da cewar tun da jijjibin safiyar talatar nan,har kawo la’asariyya wajen babu kowa hatta masu sayar da ababan makulashe da makamantan su.
Shi dai Nafi’u Gombe, ana yi masa kallon wani matashin dan siyasa ne, akewa zargin kulla boyayyiyar alaka da fadar shugaban kasa domin kawo nakasu ga jam’iyyar sa ta hadaka ADC, wacce jiga-jigan ‘yan adawa su kayi aure suka tare a cikin ta domin tunkarar zaben 2027.










