Hassan Turaki .
Tsohon minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaben 2027, matakin da ke nuna yiwuwar barkewar gagarumar fafatawar siyasa a jihar.
Gwarzo ya bayyana hakan ne a ranar 18 ga Afrilu, 2027, inda ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba mai zurfi, nazari da kuma addu’o’in neman taimako daga Allah, tare da kudurin ci gaba da hidimtawa al’umma.
Ya ce, “Bisa wannan dalili… cikin tawali’u da gaskiya na amsa kiran da aka yi min,” yana mai tabbatar da cewa zai tsaya takara a karkashin jam’iyyar APC.
A halin yanzu, kujerar na hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, lamarin da ke nuni da cewa Gwarzo na shirin kalubalantar daya daga cikin manyan jiga-jigan siyasa a Kano.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa matakin na Gwarzo na da nasaba da rikicin siyasar Kano da ke kara bayyana, musamman zargin cewa Sanata Barau ya taka rawa wajen hana nadin Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano.
Haka kuma, an hango wasu daga cikin hadiman Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a wajen bikin ayyana takarar Gwarzo, abin da ke kara karfafa zargin cewa akwai goyon baya daga wasu bangarori na gwamnatin jihar.
Ko da yake har yanzu ba a ji wata sanarwa a hukumance daga Sanata Barau ba, wannan lamari na nuna cewa ana tunkarar wata fafatawa mai zafi da daukar hankali a Kano ta Arewa gabanin zaben 2027.










