Daga Hassan R Jibrin.

Zababbun shugabanin jam’iyyar ADC na jihohi talatin da shida da Abuja, a ranar 12 ga Mayu ake sa ran rantsar da su domin gudanar da ayyukan su.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar.

Bolaji ya kara da cewa tsoffin shugabannin za su cigaba da gudanar da aikin jam’iyyar har izuwa ranar da aka ambata.

Ana ganin hakan zai kawo wani daidaito na musamman a wajen harkar gudanar da shugabanci a dukkanin jihohin kasar tare da Babban Birnin Tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here