Hassan Turaki.

Yau Lahadi 5/4/2026 zuwa 5/4/1991 Shekaru 35 da rasuwar Marigayi Sarkin Kano na 11 Sir Muhammad Sanusi na 1 Dan Sarkin Kano na 10 Abdullahi Bayero (Sarki Alhaji) Dan Sarkin Kano na 8 Muhammad Abbas Dan Sarkin Kano na 4 Abdullahi Maje Karofi Dan Sarkin Kano 2 Mallam IBrahim Dabo( Dabon Kano)a gidan Sullubawan Dabo,marigayi Sir Muhammad Sanusi na daya shine babban ‘Dan Sarkin Kano Abbas tun taso war sa mahaifin sa ya shigar da shi sha’anin mulki ya zama CHIROMAN KANO hakimin Bichi bayan rasuwar kanin mahaifin sa GALADIMAN KANO ABDULKADIR mahaifin sa ya bashi kula da NA ta Kano KANO NATIVE AUTHORITY wadda tafi kowace NA karfin tattalin arziki wannan tasa ya kara karfi bayan rasuwar mahaifin sa Sarkin Kano Abdullahi Bayero Abbas ranar 24/12/1953 ya zama Sarkin kano zamowar sa Sarkin anfara siyasa janhuriyya ta farko a shekarar 1954 wanda gidajen sarautar arewa suna goyan bayan jam’iyar NPC wato Northern People Congress mai alamar fatan ya Wanda Ahmadu Bello ko Gamji Ahmadu Rabah Wanda Dan gidan sarautar sokoto jikan Shehu usmanu Dan fodio ne da mafi akasarin jiga jigan arewa bay an zaben 1959 da samun mulkin Najeria a shekarar 1960 jam’iyar NPC ta kafa gwabnatin tsakiya CENTRAL GOVERNMENT tare da kawancen NCNC ta Dr.Azikwe kuma Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya zama Premier arewa marigayi sarkin kano Sanusi ya kara karfi kuma mai fada aji s gwabnatin Tafawa Belawa saboda kasancewar sa AMININ SARDAUNAN SOKOTO ga shi SARKIN KANO,LIMAMIN KANO,ALKALIN KANO GOVERNOR GENERAL ga ROKON ALLAH kowa tsoransa yake saboda tsarkin sa, bayan MURABUS da yayi a shekarar 29/3/1963 ya koma azare kuma KHALIFAN TIJJANIYYA SHEIK IBRAHIM NYASS ya nada shi KHALIFAN SA a NAJERIYA wannan mukami daya rike har karshen rayuwarsa da ya mutu a gidan sa na WUDIL kuma aka binne shi a GIDAN SARKI NA NASSARAWA kusa da KANO GOVERNMENT HOUSE, Allah ya gafarta masa, Rubutawa Musa Muhammad Inuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here