EDITA.

Jam’iyyar ADC tayi kira ga yan Nigeria da su mallaki katin zama cikakken Dan Jam’iyar.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin yada labarai na jam’iyyar tace cikin mintuna biyu kacal mutum zai iya mallakar katin sa na zama halastaccen dan jam’iyya ta hanyar amfani da da wayar salula.

Jigo a jam’iyyar ADC Kuma daya daga cikin mambobin kwamitin yada labarai na jam’iyyar Dr. Ladan Salihu ne ya sanar da hakan.

Ladan ya kara da cewa, akwai bukatar yan Nigeria musamman magoya bayan jam’iyyar su kwantar da hankalin su dangane da dambarwar da ake fama da shi cikin wannan kwanakin, yana me cewa komai zai wuce cikin sauki.

A karshe yayi kira ga al’uma da su dage da addu’a da Kumar nema wa kasa zaman lafiya da shugabanci na gari.

Danna wannan adireshi domin yin rijistar jam’iyyar ADC yanzu https://adcregistration.ng ka mallaka yanzu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here