Jafar Ibrahim.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya janye karar da ya shigar da alkalin babbar kotun Majistire bisa zargin take ‘yancinsa, inda ya nemi a biya shi Naira biliyan 1 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Lauyan sa, Ugochukwu Nnakwu, ne ya sanar da kotu hakan a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik lokacin da aka kira shari’ar domin sauraron bukatar da suka gabatar.
Matakin janye karar ya biyo bayan abin da mai shari’a ta lura da shi, inda ta nuna akwai gibi a cikin karar saboda rashin fayyace sunan alkalin majistare da aka kai kara a matsayin wanda ake kara na biyu.
A zaman kotun, lauyan El-Rufai ya roki kotu da ta cire sunan alkalin daga cikin wadanda ake kara, tare da kuma soke bukatar da suka gabatar a baya.










