Hassan Turaki.

Kungiyar Mataimaka na Musamman ga Shugabannin Kananan Hukumomi kan Kafofin Sadarwa na Zamani, reshen Jihar Jigawa, ta sanar da kammala zaben sabbin shugabanninta, biyo bayan karewar wa’adin shugabancin rikon kwarya da ya gabata.An gudanar da wannan zabe ne cikin lumana ta hanyar sasanto bisa ga hadin kai da fahimtar juna, Hakan ya biyo bayan takarda Mai dauke da sa hannun magatakardan Kungiyar Abubakar Bello Baba Gwaram inda aka zabi wadannan mutane domin jagorantar kungiyar: 1. Abba Maigoro (Malam Madori) Shugaba 2. Salisu Sani (Kazaure) Mataimakin Shugaba 3. Abubakar Bello Baba (Gwaram) Sakatare 4. Abbakar Musa (Gagarawa) Ma’aji 5. Yusuf Miga (Miga) Sakataren Kudi 6. Engr. Ahmad Abdullahi (Kiyawa) Sakataren Tsare-tsare 7. Alh. Abbas Suletankarkar PRO 8. Malamin Business (Kaugama) Sakataren Walwala 9. Abubakar Idris (Guri) Mai Ba da Shawara kan Shari’a 10. Yahaya Dankoli (Taura) Mataimakin Sakatare 11. Abubakar Haruna Bala (Hadejia) Mataimakin PRO 12. Ishaq Fanini (Birnin Kudu) Mai Binciken Kudi (Auditor)Kungiyar ta bayyana cewa sabbin shugabannin za su fara aiki nan take, tare da kudurin ci gaba da inganta ayyukan kungiyar da kuma kare muradun dukkanin mambobinta.Haka kuma, kungiyar tana mika godiya ta musamman ga tsohon shugaban rikon kwarya, Abdulrazak Adamu, bisa irin jajircewa, kokari da kyakkyawan jagoranci da ya nuna a lokacin da yake rike da amanar jagoranci. Kungiyar ta yaba da gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ciyar da kungiyar gaba.A jawabin sa sabon shugaban CmrD. Abba Maigoro yayi alkawarin kawo sauyi tare da nuna cigaban aiyukan Gwamnatin jiha da Kuma kananan hukumomi a kafofin sada zumunta na zamani.

Source Alh. Musa Muhammad

Information officer malam madori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here