Hassan R Jibril.
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, tayiwa kungiyar Kwankwasiyya t a Karamar Hukumar Dawakin-Kudu garanbawul a wasu kwamatocin kungiyar.
Kwamatocin da abin ya shafa sune na Lafiya Jari,Kano Proper, da CRC.
Sauran sun hadar da na Kwamatin Koli da Ulama. Dr Halliru Bilyamin Gano,shine sabon shugaban Kano Proper yayin da Farouk Tijjani Dawaki ya zamo Sakatare.
A bangaren CRC kuwa, Engineer Munir Nuhu shine sabon Shugaba shi kuwa Alhaji Abdurrahaman Tasi’u Gano Sakatare, Malama Balaraba Hamisu ita ce Shugabar Mata.
Alasan Burbur Tsakuwa shine Shugaba a Kwamatin Option ‘A’, Malam Sabo Dan-Magori Sakatare,kujerar Shugabar Mata a yanzu Malama Ladidi ce.
Kwamatin Koli na Karamar Hukumar yanzu yana karkashin kulawar Dr Mujahid Guda Dawaki tare da Alhaji Usman Ma’aji Tamburawa, Malam Abba Ado Jido shine Mataimakin Shugaba Dr Tahir Gwani Dawaki da Mai Sadi Tsakuwa za su kula da Kwamatin Ulama na kungiyar.










