Hassan Turaki.

Imam Abdurahman Hadejia ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake gabatar da lakca a sakatariyar Yan Jaridu ta jihar Jigawa dake G9 quarters a birnin Dutse, Wanda kungiyar yan jaridu ta jihar Jigawa hadin gwiwa da ofishin sakataren gwamnatin jiha suka dauki nauyi.Malam yace Annabi S.A.W yace Ka ambaci dan uwanka da abinda yake ki wannan shine giba.Mal. Abdurahman yace babu inda ALLAH da kansa yayi kwatancen cin naman mutum sai akan giba saboda girman laifin.Wanda akazo masa da zancen wani Kuma ya dakatar da zancen tabbas ALLAH zai bashi gidan aljannah kamar yadda yayi alkawari Inji malam.A cigaba da bayani dangane da zunubin zancen wani, Mal. Yace manzon ALLAH S.A.W yace da mutum yayi zancen wani gara yaci naman mushen jaki yafi alkhairi a wajen shi.A cikin bayanin sa yace dauko zancen wani domin kayi masa batanci shine annamimanci wanda girman laifin yafi na giba, na daga cikin laifin da tun a duniya ake baiwa mutum uquba da shi zuwa kabarin sa Kafin ranar hisabi.Ya kara da cewa giba da annamimanci da rashin kula da tsarki yana jawo azabar kabari.Abubuwa biyar sune suke haddasa giba wanda sun hada da Hassada da fushi da mutane da raunin Imani da zama da mutanen banza sai Kuma yawan zance.Abubuwa biyar da giba da annamimanci ke haddasawa sun hada da Kisan aure, da Janke zumunci, da sai Kuma yawan wasi-wasi da rashin yarda a cikin al’uma sai Kuma kiyayya a cikin al’uma.A karshe malam yace hanyoyin magance giba da annamimanci shine kiyaye tauhidi, da tuna mutuwa da Kuma yawan zikiri sai kaurace wa guraren da ake zancen mutane, da hani a yayin da aka fara giba da annamimanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here