Daga Hassan R Jibril.

Kamar yadda gidan talabin na Channels ya labarto, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta lashe aman da tayi.

Kwanakin baya ne, hukumar bisa ‘dogaro’ da wani umarnin Kotu mai sarkakiyar fassara ta rushe shugabancin ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark.

Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Najeriya, inda ake ganin jam’iyya mai mulki ta APC na son kawowa ‘yan adawa tarnaki a zaben 2027.

A yanzu a iya cewa kanwa ta kar kwarnafi a inda hukumar ta dawo da sunayen shugabanin a shafinta na yanar gizo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here