Gwamnatin Jihar Kano tare da SSR ɗin Gwamna, Auwalu Sani Rogo, sun bai wa ƴan jarida hakuri kan zargin cin mutunci da aka yi wa wani ɗan jarida.

Hakan ya biyo bayan zaman sulhu da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kira a yau Laraba domin shawo kan matsalar.

Zaman sulhun ya samu halartar shugabannin ƴan jarida na yanar gizo ƙarƙashin ƙungiyar Kano Online Media Chapel, karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin Ma’aikatar Yaɗa Labarai, tare da wasu ƴan jarida da kuma tsohon shugaban NUJ, Comrade Abdullahi Datti Arzai.

Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishina Waiya ya bukaci SSR Rogo da sauran jami’an gwamnati da su rika kyautata mu’amala da ƴan jarida domin ci gaban Jihar Kano.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da aiki kafada da kafada da kafafen yaɗa labarai, yana mai amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

A nasa bangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abdulƙadir Dangambo, ya gode wa kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar, yana mai bayyana cewa irin wannan hali da Auwalu Rogo ke nunawa ga ƴan jarida ba wannan ne karo na farko ba.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da jan hankalin jami’an gwamnati da su fahimci muhimmiyar rawar da ƴan jarida ke takawa a cikin al’umma da kuma irin darajar da suke da ita a duniya baki ɗaya.

Zaman sulhun ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na cikin gida da na ƙasashen waje suka yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare da bai wa gwamnatin jihar Kano wa’adin sa’o’i 24 da ta ɗauki mataki, ko kuma su tafi gaban kotu.

An bayyana fatan cewa wannan sulhu da aka cimma zai zama silar gyara halayen SSR Rogo wajen mu’amala da ƴan jarida da kuma al’umma baki ɗaya.

https://www.facebook.com/share/p/1CHDnpFoGA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here