Abdullahi Aminu Jahun.

Hukumar Jindadin Alhazai ta jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kammala aikin tantance lafiyar maniyatan aikin Hajjin bana, wanda hakan wani babban matakin ne a ayyukan aikin Hajjin 2026.

Darakta janar na hukumar Alhaji Ahmad Labbo ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dangane da shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Labbo ya tabbatar da cewa tawagar jami’an kiwon lafiya sun kammala aikin tantance lafiyar maniyatan da kuma duk wasu abubuwan da ake da bukata ta bangaren maniyata bisa dokokin hukumar Jindadin Alhazai ta kasa.

Darakta janar na hukumar ya kuma godewa Gwamna Malam Umar Namadi bisa samarda duk wasu abubuwan da ake da bukata domin tallafawa ayyukan hukumar.

MNT/NET/Abdullahi Aminu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here