Wakilin mu
PDP ta doke APC da sauran jam’iyyun da suka tsaya takarar shugabancin Gwagwalada a AbujaHukumar zaben Nijeriya INEC ta ayyana Mohammed Kasim na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin karamar hukumar Gwagwalada, Abuja da aka gudanar ranar Asabar.Sakamakon da INEC ta fitar ya nuna cewa Mohammed Kasim ya samu kuri’u 22,165, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Yahaya Shehu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 17,788.Sauran jam’iyyu kuwa, ADC ta samu kuri’u 1,366, yayin da APGA ta samu kuri’u 1,687.









