Daga Hassan R Jibrin.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, ya yi dan takarar Shugabancin Kasa a karkashin jam’iyyar NDC, Mr Peter Obi ya sha alwashin, idan ya samu nasara a zaben 2027 zai toshe duk wata hanya da kudaden talakawa ke zurarewa.

“Hanyoyin gudanar da mulki dole ne a takaita su. Babu yadda talakawa suna cikin rashi, masu mulki suna sharholiya. Wannan ba daidai bane” acewar sa.

Batun ire-iren wasu ofisoshi kamar na Mai Dakin Shugaban Kasa, ya ce ba matar aka zaba ba, babu wani dalilin samar da shi.”Yaki da cin hanci, abu ne mai saukin aiwatar, idan Gwamnati da gaske ta keyi,amma yanzu wasan yara da bita da kulli ake wa abokan adawa..

Duk tsantseninka, idan baka APC sai an kirkiro laifi an zarge ka shi.Amma idan kana APC ka zama waliyyi duk barnar da kayi ga talakawa”Ya kuma jadda batun aniyarsa kan zangon wa’adi daya.

Domin samar da sahihin tsari mai cike da muradun ‘yan Kasa, ya fi shekaru ashirin na son zuciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here