Daga Hassan R Jibrin
Wani tsohon sojan Najeriya kuma dan kasuwa,Alhaji Auwalu Soja, ya nuna bacin ransa akan da halin da yankin Arewa ya tsinci kansa a halin yanzu.
A wani sakon sauti da jaridar Guarantee ta samu, ya jawo hankulan manyan yan siyasar yankin da su yi karatun tanatsu ta bin shawarar da Janar Badamasi Babangida ya bayar domin kaucewar rugujewar yankin.
“Muna da arziki, amma talauci da firgici na rashin kwanciyar hankali nema suke su tare a yankin” acewar Auwalu Soja.
Ya kuma yi kira ga matasa da suyi duba ga yadda ake kokarin maida su ‘yan kwaya domin biyan bukatun wasu maras sa kishi.
A karshe ya bukaci malaman addini dake yankin ,suyi tsayin daka kamar a 2023, domin ceto yankin daga halin da ake ciki.










