Daga Hassan Turaki .
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al’uma ta jihar Jigawa, JPCACC, da Cibiyar Kasa ta Nazarin Majalisa da Dimokuradiyya, NILDS, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da nufin karfafa karfin hukumomin domin inganta gaskiya da rikon amana, da kuma tabbatar da mulki na dimokuradiyya a Najeriya.
An gudanar da bikin rattaba hannun a dandalin din-din-din na cibiyar dake Abuja.
Yayin jawabi a wurin, Shugaban Zartarwa na hukumar a nan jihar jigawa JPCACC, Barrista Salisu Abdu, ya bayyana wannan mataki a matsayin sakamakon tattaunawa da ta fara a watan Afrilu na shekarar 2026 lokacin ziyarar girmamawa da suka kai NILDS.
Ya kara da cewa hukumomin biyu sun gano bukatar yin aiki tare a fannin bunkasa karfi, horar da ma’aikata, bincike, da karfafa hukumomi.
“Mun dauki nauyin magance korafe-korafe na jama’a, hana cin hanci, karfafa zaman lafiya ta hanyar kwarewa, gaskiya, rikon amana da ci gaba da inganta ayyukan hukumar mu,” in ji Barrista Abdu.
Yace, wannan yarjejeniyar ba wai yarjejeniya ce ta takarda kawai ba, sai dai tsarin dabaru ne na ci gaba mai dorewa. Zai samar da hadin gwiwa a fannoni kamar horo na karfafa karfi, ilimi na manyan jami’ai, horo na musamman, bincike, tsara manufofi, tallafin fasaha, da musayar ilimi.
Shugaban ya bayyana kyakkyawar fata cewa wannan kawance zai baiwa jami’an Hukumar damar koyon sabbin dabaru na gudanar da aiki, kula da dabi’a da mutunci, dabaru na bincike domin warware takaddama, da kuma dabarun yaki da cin hanci.
Wannan zai inganta yadda ake bawa mutanen Jihar Jigawa cikakkiyar damar morar aikin Jpcacc.Barrista Abdu ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, FCA, bisa goyon bayan da yake bayarwa hukumar wajen bunkasa karfin Ma’aikatar.
Daga bangaren sa, Darakta Janar na NILDS, Farfesa Abubakar O. Sulaiman, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa kafa wannan Hukuma domin inganta gaskiya, rikon amana a dimokuradiyya.
“Kalubalen mu ba rashin dokoki ko albarkatu ba ne, sai dai aiwatar da dokokin da muke dasu ta hanyar kwararru masu nagarta da rikon amana wajen kula da dukiyar jama’a,” in ji Farfesa Sulaiman.
Ya ce wannan yarjejeniya zai karfafa hukumomin ta hanyar bada horo na musamman, musayar ilimi da koyon sabbin dabaru na gudanar da aiki.
Haka kuma an yaba wa tawagar fasaha ta JPCACC da NILDS bisa jajircewarsu.JPCACC ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da aiwatar da dukkan abubuwan da ke cikin yarjejeniyar domin samar da sakamako mai ma’ana da karfafa aikin a hukumance.










