Naziru Hamisu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa duk da ra’ayoyi mabambanta da ake da su a kai, Nijeriya na buƙatar shugabanni masu nagarta da ƙwarewa irin Nasir Ahmad El-Rufai domin ci gaban ƙasa.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga El-Rufai, inda ya jajanta masa kan wannan rashin da ya same shi.
A yayin ziyarar, ya jaddada cewa ƙasar na bukatar shugabanni masu hangen nesa, jajircewa da kuma iya tafiyar da al’amura cikin gaskiya da riƙon amana.
Ya ce, duk wanda ya san gaskiya, zai amince cewa irin rawar da El-Rufa’i ya taka a fannoni daban-daban, musamman a lokacin da yake gwamnan Jihar Kaduna, abin koyi ne ga sauran shugabanni.
2027: I have never met Atiku in Mecca – Northern governor debunk
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da al’umma da su mayar da hankali kan abin da zai haɗa kan ƙasa maimakon rarrabuwar kawuna, yana mai cewa haɗin kai da shugabanci nagari ne ginshiƙan ci gaba.
A nasa ɓangaren, Nasir Ahmad El-Rufa’i ya gode wa Shettima bisa wannan ziyara da kuma kalaman tausayawa da ƙarfafa gwiwa da ya yi masa, inda ya ce hakan na nuna zumunci da haɗin kai a tsakanin shugabanni.
Ziyarar ta samu halartar manyan ‘yan siyasa da jiga-jigan gwamnati, inda aka yi addu’o’i na musamman domin marigayin da kuma fatan samun zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.










