DAGA: AUWAL ISHAQ SANKARA.

An ƙaddamar da sabon ofishin Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), wanda aka fi sani da Civil Defence (Jar Kwala), a garin Sankara da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Samar da ofishin ya samu ne sakamakon ƙoƙarin Sankara Elders Forum ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Malam Sani Muhammad Adamu Sankara, a wani mataki na ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a garin Sankara da ƙauyukan da ke kewaye.

Da yake jawabi yayin taron ƙaddamarwar, Malam Sani Muhammad Adamu Sankara ya bayyana cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, yana mai jaddada cewa samar da wannan ofishi zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yabawa Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa bisa amincewa da buɗe sabon ofishin, tare da jinjinawa al’ummar Sankara bisa haɗin kai da suka nuna wajen tara kuɗi da bayar da gudummawa domin ganin an kammala aikin.

A cewarsa, wasu daga cikin al’umma sun bayar da shaguna domin amfani da su a matsayin ofishi, yayin da wasu kuma suka tallafa da kuɗi wajen gyaran ginin da samar da kayan aikin da ake buƙata. Ya yi addu’ar Allah Ya saka wa kowa da alheri.

Shi ma da yake nasa jawabin, mai magana da yawun Sankara Elders Forum, Abdulhadi Yusuf Sankara, ya ce haɗin kai da karamcin al’ummar Sankara ba sabon abu ba ne, domin sun saba da bayar da gudummawa wajen ci gaban garinsu.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta riga ta miƙa dukkan kayan aikin da ake buƙata ga sabon Divisional Officer (D.O.) da aka tura garin Sankara domin fara aiki a hukumance.

A nasa jawabin, sabon D.O. na Civil Defence ya nuna matuƙar farin cikinsa da irin goyon baya da al’ummar garin suka bayar.

Ya ce wannan abin koyi ne ga sauran al’ummomi, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro haɗin kai da kuma sanar da su duk wani abu da zai taimaka wajen kare zaman lafiya.

Ya tabbatar da cewa jami’an Civil Defence za su gudanar da aikinsu cikin adalci da gaskiya, tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An kammala taron ne da addu’o’in fatan alheri da kuma kira ga al’ummar Sankara da su ci gaba da ba jami’an Civil Defence cikakken haɗin kai domin samun ingantaccen tsaro da dorewar zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here