Imrana Galaje.
Kungiyar kwallon kafa ta Warinje FC da ke Bauchi ta sanar da gudanar da manyan sauye-sauye a bangaren gudanarwa da horaswa, a matsayin wani mataki na sake tsara kungiyar gabanin sabon kakar wasa.Wannan na cikin sanarwar da Shugaban Kungiyar, Musa Abdullahi Mai-Auguda, ya fitar ranar Alhamis.
Hukumar ta bayyana cewa ta sallami dukkanin ma’aikatan masu horaswa da sauran jami’ai, bayan tantance yadda kungiyar ta gudanar da kakar da ta gabata da kuma shirye-shiryen da take da su na gaba.*Manyan Sauye-Sauye* *Sallamar Jami’ai*: An sallami Daraktan Wasanni, Abdullahi Adamu, da Manajan Kungiyar, Bala Garba, daga mukamansu nan take.
Rusa Ma’aikata: Hukumar ta rusa dukkanin ma’aikatan masu horaswa da sauran jami’an kungiyar, a matsayin wani bangare na cikakken sauyi da aka tsara domin cimma burin kungiyar na dogon lokaci. Sabon Kocin Riko: An nada Saidu Abdullahi, wanda aka fi sani da Coach Yellow”, a matsayin kocin riko. Zai jagoranci atisaye da shirye-shirye har sai an nada kocin dindin.
Hukumar ta umarci dukkanin ‘yan wasan Warinje FC da ke Bauchi da su koma atisaye nan take, yayin da ake fara aikin sake gina kungiyar.Bugu da kari, ta ba da umarnin a mayar da dukkan kayayyakin kungiyar da ke hannun tsoffin jami’ai ga Rabiu Abdullahi, wanda aka fi sani da “Rangers” Hukumar ta kuma gabatar da sabon tsarin sadarwa, inda ta ce duk wata takardar hukuma dole ne ta kasance da sabon takardar wasiku ta kungiyar.
Sannan Shugaban Kungiyar/CEO ko Janar Manaja ne kadai za su sanya wa hannu.
Warinje FC ta ce za a sanar da sabbin jami’ai da ma’aikatan horaswa nan ba da jimawa ba, yayin da ake ci gaba da shirin sauye-sauyen.A karshe hukumar ta yaba da gudunmawar tsoffin jami’an, inda ta ce: _”Muna yi muku fatan alheri a ayyukanku na gaba. Dukkanmu ‘yan uwa ne a cikin gidan Warinje FC.”









