Daga Hassan Turaki.
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un.” Ubangiji Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Zamfara, Alhaji Ahmed Liman, rasuwa.
Marigayin ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya jefa ma’aikatan gwamnati da ‘yan uwansa cikin alhinin rashin sa.
Ana sa ran gudanar da sallar janazarsa a yau Talata da karfe 4:30 na yamma a Masallacin Jumu’a na Kanwurin Sarki dake Gusau, In sha Allah.
Alhaji Ahmed Liman ya yi aiki na tsawon shekaru a hidimar jihar Zamfara, inda ya rike mukamin Shugaban Ma’aikatan Jihar tare da bayar da gudummawa wajen gudanar da harkokin gwamnati.
Abokan aikinsa da ‘yan uwansa sun bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, mai bin doka da oda, kuma wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar al’umma.
Dangi, abokan arziki da jami’an gwamnati ana sa ran za su halarci janazarsa domin yi masa addu’ar rahama.
Allah Ya jikansa da rahamarsa, Ya gafarta masa zunubansa, tare da sauran musulmin da suka riga mu gidan gaskiya. Allahumma Amin, Ya Rabbil ‘Alamin.










