Daga Hassan R Jibrin

Ga dukkan alamu, wani sabon yanayi a siyasar Najeriya sai kara bayyana yake a cikin da’irar harkokin siyasar kasa.

2027, zata zo ne da ‘yantakarar Shugaban Kasa daga shiyoyi biyar, hakan ga dukkan alamu zai rage siyasar bangaranci.

Daga Kudu maso Yamma, Shugaba mai ci, Bola Tinubu na jam’iyyar APC tare da Gwamna Seyi Making a APM. Shiyyar Kudu maso Kudu, Mr Omoleye Sawore a ACC sai PDP da zata mika tikiti ga Mr Goodluck Ebele Jonathan.

A bangaren Kudu maso Gabas, ‘yan takarkari guda biyu ne, Peter Obi na NDC sai Mr Donald Duke inda PRP ta sahalewa domin yi mata takara.

A daukacin fadin shiyyar Arewa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar shine daya tilo, wanda jam’iyyar sa ta ADC ta lamunce wa takara bayan lashe zaben fidda gwani.

Ko acikin wannan sabon tsarin siyasar, bangaranci zai iya taka wata muhimmiyar rawa ? Ko addini ka iya yin tasiri ? Idan kuma zai yi, ga wanne dan takara ne zai ci moriya ?Lokaci kadai zai fassara yanayin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here