Daga Hassan R Jibrin.
Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a Abuja wanda Mai Shariya Peter Lifu ke shugabanta, tayi watsi da wata kara dake gaban ta kan bukatar hana tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, dawowa fagen siyasar Najeriya.
Wani lauya mai suna Jideobi ne ya shigar da bukatar a gaban kotun.
Mai Shariya Peter Lifu a hukuncin sa, ya ce mai korafin ya gaza kawo gamsassun hujjoji ga Kotu, inda tayi watsi da karar bisa hujjar cewa tuni Babbar Kotun Tarayya dake Yenagoa da kuna Kotun Daukaka Kara duk sun yi musharaka cewar babu wata doka da zata hana wanda akai kara shiga harkokin siyasa ko tsayawa takara.
Kotun ta bukaci mai kara da ya biya wanda yayi karar Naira miliyan ashirin da kuma wata Naira miliyan daya ga Babban Lauyan Kasa
Tun farko, Kotun ta ki amincewa da bukatar mai kara domin nuna rashin sha’awar ci gaba da shariyar, amma Kotu ta nuna cewa gabanta ba wurin wasa bane










