Daga Hassan R Jibrin


Hukuma mai kula da kwalejojin ilmi ta kasa, ta amincewa Kwalejojin Ilmi da su fara shirye-shiryen bayar da shaidar karatun digiri kai tsaye ba tare da hadin gwuiwa da wata Jami’a ba.


Shugabar Hukumar, Dr Angela Ajala ta sanar da hakan,biyo bayan aiwatar da sabbin tsare-tsaren inganta Makaratun Kwalejojin Ilmi.
A kwanakin baya ne, Dr Ajala ta ankarar da samun wagegen gibin kwararrun malamai a makarantun kasar da suka kai kusan dubu dari biyu.


Dr Ajala ta sha alwashin kawo karshen karancin kwararrun malamai ta hanyar inganta Kwalejojin ilmin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here